Kungiyar Francophonie Na Gudanar Da Taro A Kasar Armenia
kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransa a duniya francophonie na gudanar da taron koli karo na 17 a birnin Ervan na kasar Armenia, da ya samu halartar shugabannin kasashen duniya cikin su kuwa har da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Kungiyar da ke sa ido kan ci gaban harshen Faransaci a duniya ta fitar da rahotonta na shekaru hudu, da ke bayyana harshen a matsayin na 5 a duniya.
A shekara ta 2014 an kiyasta cewa, masu amfani da wannan harshe su kai milyan 274 a duniya, to sai dai a halin yanzu adadinsu ya haura zuwa milyan 300 .
Duk da wannan cigaba da yaren na faransanci ya samu cikin shekaru hudu, hakan na nufin cewa Faransanci na matsayi na biyar ne a duniya baya ga harshen Mandarin, Ingilishi, Spaniyanci da kuma Larabci da ke gabansa.
Rahotan dai na nuni da cewa a halin yanzu kasashen 32 ne ke amfani da Fanransanci a matsayin harshen hukuma, duk da cewa shi ne na hudu da aka fi amfani da shi wajen gudanar da binciken kimiya da sauran hanyoyin sadarwa na zamani.
Yawan masu amfani da harshen na Faransanci a duniya ya samo asali ne sakamakon karuwar jama’a musamman a kasashen Afrika renon Faransa, inda kashi 68% ke zaune a nahiyar a yankin Kudu da Sahara na nahiyar Afrika, sai kuma 22% daga Arewancin nahiyar.
A Congo-Brazzaville ne aka fi amfani da harshe da 59%, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a matsayin ta biyu da 50%, sai Côte d’Ivoire da 33%, Sénégal 26%, Mali da Tchad kowanne 17% yayin Niger ke da 13%.