Hari Da Wuka Ya Ci rayukan Mutum daya
"Yan sandan birnin London sun sanar da cewa harin da aka kai da wuka ya yi sanadin mutuwar mutum daa da kuma jikkata wani daya
Sanarwar 'yan sandan ta ce wani mutum ne dan shekaru 22 aka soke shi da wuka, ya kwanra dama, yayin dani dan shi ma dan shekaru 22 ya jikkata kuma tuni an kai shi asibiti domin samun magani.
"Yan sandan sun sanar da bude bincike domin gano wanda ya kai hari da kuma dalilinsa.
Wani rahoton yan sandan ya ambaci cewa a ciki shekara guda an kai hare-hare ta hanyar amfani da wuka har sau 40, da 147 a fadin kasar, wanda shi ne mafi girman harin da aka kai a cikin shekaru bakwai na bayan nan.
A cikin birnin London kadai, wanda ake dauka a matsayin daya daga cikin birnanen da aka fi aikata laifuka a cikin kasar, an kai hari da wuka har sau 1299 a cikin watanni 4 na farkon shekarar da ake ciki.
Wata kididdigar ta ce a cikin 2018 kadai an kashe mutane 104 a cikin London ta hanyar amfani da farin makami, sai kuma wasu 10 da aka kashe da albarusai.