An Cabke 'Yan Ta'addar ISIS 6 A Moscow
Cibiyar tsaron kasar Rasha ta sanar a daren jiya juma'a cewa jami'an tsaro sun samu nasarar cabke 'yan ta'addar ISIS 6 a Mascow babban birnin kasar
Sanarwar ta ce 'yan ta'addar da aka kama 'yan kasashen Asiya ta tsakiya ne kuma suna karbar umarni daga manyan kwamondojinsu dake kasar Siriya, kuma bisa bayyanan sirrin da aka samu, 'yan ta'addar na shirye-shiryen kai harin ta'addanci ne a kasar ta Rasha.
Bayan gudanar da bincike a gidajen 'yan ta'addar, an samu makamai na zamani tare kuma da na'urorin sadarwa gami da umarni dasa bama-bamai a cikin kasar.
A cikin watanin da suka gabata, kasar ta Rasha ta fuskanci hare-haren ta'addanci a wasu sasan kasar.
A tsakiyar shekarar 2015 ne kasar Siriya ta bukaci taimakon Rasha wajen yakar 'yan ta'addar dake samun goyon wasu kasashen Larabawa gami da wasu manyan kasashen Duniya, inda kasar ta Rasha ta tura Dakarunta na sama,suka fatattaki 'yan ta'addar daga sama, su kuma Sojojin Siriya gami da dakarun sa kai gami da kungiyoyin gwagwarmaya suke kai musu farmaki daga kasa.lamarin da ya sanya aka samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'adda da magoya bayansu.