Amurka : Dan Bindiga Ya Hallaka Mutane A Wurin Ibadar Yahudu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33813-amurka_dan_bindiga_ya_hallaka_mutane_a_wurin_ibadar_yahudu
'Yan sanda a Amurka sun samar da mutuwar mutane da dama da kuma raunanar wasu a yayin da wani dan bindiga ya bude wuta a wani wurin ibadar yahudawa a birnin Pittsburgh dake yankin Pennsylvanie a daidai lokacin da jama'a ke ibada.
(last modified 2018-10-27T13:57:34+00:00 )
Oct 27, 2018 13:57 UTC
  • Amurka : Dan Bindiga Ya Hallaka Mutane A Wurin Ibadar Yahudu

'Yan sanda a Amurka sun samar da mutuwar mutane da dama da kuma raunanar wasu a yayin da wani dan bindiga ya bude wuta a wani wurin ibadar yahudawa a birnin Pittsburgh dake yankin Pennsylvanie a daidai lokacin da jama'a ke ibada.

Dan bindigan dai wanda ba'a bayyana manufarsa ba ya bude wuta kan yahudawan dake ibada kafin ya mika kansa ga 'yan sanda, a cewar kakakin 'yan sanda yankin.

lamarin dai ya auku ne a anguwar Squirrel Hill dake birnin Pittsburgh, dake zaman wuri mai dadaden tarihi ga al'ummar yahudawa dake rayuwa a yankin dake arewa maso gabashin Amurka.

Kwamandan 'yan sandan yankin ya ce akwai 'yan sanda uku dake da matsayin ofisa da suka raunana sakamakon harbin dindiga.

Gidan talabijin na CNN ya rawaito cewa mutum akalla hudu ne suka mutu a lamarin, a yayin da shugaba Donald Trump ya danganta lamarin da abun takaici, tare da shan alwashin daukar mataki don kawo karshen ire iren wadanan ayyuka da ya ce basu da wuri a kasarsa dama duniya baki daya.