Akon Ya Sanar da Cewa Zai Tsaya Takarar Shugabancin kasar Amurka
Fitaccen mawaki dan kasar Amurka kuma dan asalin kasar Senegal Aliaume Damala Badara Akon Thiam ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar ta Amurka a zaben 2020.
Shafin yada labarai na Today 24 ya bayar da rahoton cewa, Akon fitaccen mawaki dan kasar Amurka kuma dan asalin kasar Senegal ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar Amurka ne domin kalubalantar shugaba mai ci yanzu.
Akon dai ya shahara wajen nuna tsananin kiyayya da salon siyasar wariya da bangaranci irin ta Donald Trump, kuma ya sha alwashin cewa idan har ya lashe shugabancin Amurka, to za a kawo karshen irin wannan bakar siyasa ta Trump a Amurka.
A cikin shekarun baya dai Akon ya gina makarantu a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afrika, domin taimaka ma marassa galihu.