Amurka Ta Bukaci Saudiyya Ta Mika Gawar Kashoogi Ga Iyalansa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33895-amurka_ta_bukaci_saudiyya_ta_mika_gawar_kashoogi_ga_iyalansa
Ma'aikatar harkokin wajen Amukr ta bakin mataimakin ministanta ta ce; Wajibi ne ga mahukuntan Saudiyya da su mika gawar Kashogi ga iyalansa cikin gaggawa
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 02, 2018 15:38 UTC
  • Amurka Ta Bukaci Saudiyya Ta Mika Gawar Kashoogi Ga Iyalansa

Ma'aikatar harkokin wajen Amukr ta bakin mataimakin ministanta ta ce; Wajibi ne ga mahukuntan Saudiyya da su mika gawar Kashogi ga iyalansa cikin gaggawa

kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato RObert Palladino yana cewa; Ya zama wajibi ne a a bayyana yadda aka yi da gawar Jamal Kashoogi sannan kuma a mikawa iyalansa domin yi ma sa sutura.

A kasar Turkiya kuwa ma'aikatar shari'ar kasar ta bukaci Saudiyyar da ta bayyana mata inda ta kai gawar dan jaridar da ta kashe a cikin karamin ofishin jakadancinta da yake birnin Istanbul.

 A ranar 2 ga watan Oktoba ne dai Jamal Kashoogi ya shiga cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da yake a birnin Stanbul, ba tare da ya fito daga ciki ba. Sai a ranar 20 ga watan na Oktoba ne dai Saudiyyar ta yi ikirari da cewa wasu fandararrun ma'aiaktanta ne su ka kashe shi.

Kasashe da dama da kungiyoyin kasa da kasa sun yi Allah wadai da kisan na kashoogi tare da yin kira ga Saudiyya da ta fito da gawarsa.