Amurka Ta Yarde Wa Kasashe 8 Sayan Man Fetur Din Iran
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33900-amurka_ta_yarde_wa_kasashe_8_sayan_man_fetur_din_iran
Amurka ta sanar a hukumance da matakinta na maido da duk jerin takunkumankanta Iran, watanni shida bayan da shugaban kasar Donald Trump ya sanar da janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Nov 03, 2018 06:38 UTC
  • Amurka ta kuma ce sassaucin nan da ya shafi magunguna da kuma abunci, yana nan daram
    Amurka ta kuma ce sassaucin nan da ya shafi magunguna da kuma abunci, yana nan daram

Amurka ta sanar a hukumance da matakinta na maido da duk jerin takunkumankanta Iran, watanni shida bayan da shugaban kasar Donald Trump ya sanar da janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

 Sanarwar da fadar gwamnatin Amurka ta fitar ta ce jerin takunkuman wadanda zasu kasance mafi tsanani, zasu fara aiki ne a ranar Litini 5 ga watan Satumban nan.

Saidai sanarwar ta ce Amurka ta yarde wa wasu kasashe takwas dasu ci gaba da sanya man fetur daga Iran, amma na tsawan watannin shida masu zuwa.

Koda yake sanarwar bata zayyana kasashen ba, amma wasu kasashe kamar su Iraki da Turkiyya, ta bakin ministocin harkokin wajen kasashensu sun ce suna daga cikin jerin kasashen, a yayin da kuma ake hasashen kasashen Indiya da Koriya ta Kudu da kuma Japon da China suma zasu samu wannan damar.

Amurka ta ce duk kasashen da ta yarde su ci gaba da sayan man fetur din na Iran, kawayenta ne ko kuma wadanda take hulda dasu a wasu bangarori.

Babu dai wata kasa daga kasashen turai da wannan matakin ya shafa.

Amurka ta kuma ce sassaucin nan da ya shafi magunguna da kuma abunci, yana nan daram.

A cikin wata sanarwa ta bai daya da suka fitar, kungiyar tarayya Turai, da Faransa da Jamus da Biritaniya sun nuna bakin cikinsu dangane da wannan matakin na Amurka na maido da takunkumanta kan Iran.