Macron: Shugabannin Kasashe 60 Za Su Halarci Zaman Taron Paris
Mahukuntan kasar Faransa sun bayar da sanarwar cewa, shugabannin kasashe 60 ne za su halarci taron sulhu a birnin Paris na kasar Faransa.
Shafin Russia Today ya bayar da rahoton cewa, Emmanuel Macron shugaban Faransa ya sheda cewa, shugabannin kasashe 60 ne aka ajiye magana da su wadanda za su halarci taron sulhu a birnin Paris da a za a gudanar.
Wannan taro dai ana gudanar da shi ne duk shekara-shekara domin tunawa da kawo karshen yakin duniya na farko, wanda kuma wannan shi ne karo na dari da za a gudanar da taron, wanda zai samu halartar shugabannin kasashe da suka hada da Vladimir Putin na Rasha, Trump na Amurka da sauransu.
Za a gudanar da taron ne a ranar 11 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki, kuma gwamnatin faransa ce za ta dauki bakuncin taron.