Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 12 A Amurka
Rahotanni daga Amurka na cewa wani dan bindiga ya hallaka mutum 12 a wata mashaya dake kusa da birnin Los Angeles a kudandin California.
Ofishin ‘Yan Sandan yankin ya ce, al’amarin ya faru ne a dai dai lokacin da daliban wata makarantar Kwaleji ke gudanar da biki a cikin daren ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 12 da kuma jikkatar wani adadi mai yawa.
Bayanai sun ce dan bindigan shi ma ya mutu a lamarin, saidai babu karin haske ko kashe kansa ya yi da kansa ko kuma jmai'an tsaro ne suka harbe shi.
Ba'a dai ga tantance dan bindigar ba ko kuma manufarsa, amma ganau sun shaida cewa mutumin yana sanye da bakar riga da kuma dogon gemu, dauke kuma da babbar bindiga.
'Yan sanda yankin sun ce ana cikin gudanar da bincike kan ko lamarin na da alaka da ta'addanci ko kuma a'a.