Ministan Sufurin Birtaniya Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34016-ministan_sufurin_birtaniya_ya_yi_murabus
Ministan sufurin Birtaniya ya yi murabus kan batun ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai.
(last modified 2018-11-10T05:55:24+00:00 )
Nov 10, 2018 05:55 UTC
  • Ministan Sufurin Birtaniya Ya Yi Murabus

Ministan sufurin Birtaniya ya yi murabus kan batun ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai.

Gidan talabijin din kasar Birtaniya ya habarta cewa a jiya juma'a Ministan sufurin kasar Jo Johnson ya nuna rashin amincewarsa kan tsarin Piraministar kasarTheresa May  na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai, lamarin da ya sanya yin murabusa daga kan mukaminsa.

 Jo Johnson ya ce tsarin da Piraministar ta gabatar nada fuska biyu, kuma a halin da ake ciki kasar na cikin mawuyacin hali kamar na bayan yakin Duniya na biyu.

Johnson wanda dan uwa ne ga Boris Johnson da ya yi Murabus daga mukamin sakataren harkokin wajen kasar cikin watan Yuli ya kuma bukaci sake gudanar da zaben raba gardamar ficewar kasar daga EU.

Wannan, shi ne murabus na uku da ministocin kasar Birtaniyar suka yi a gwamnatin Piraminista Therasa May.