Rasha Ta Bayyana 'Isra'ila' A Matsayin Ummul Aba'isin Din Rikicin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34065-rasha_ta_bayyana_'isra'ila'_a_matsayin_ummul_aba'isin_din_rikicin_gaza
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin ummul aba'isin din rikicin da a halin yanzu ya kunno kai a Gaza tana mai zargin Isra'ila da haifar da yanayin rashin tsaro a yankin Gabas ta tsakiya.
(last modified 2018-11-14T03:04:48+00:00 )
Nov 13, 2018 11:21 UTC
  • Rasha Ta Bayyana 'Isra'ila' A Matsayin Ummul Aba'isin Din Rikicin Gaza

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin ummul aba'isin din rikicin da a halin yanzu ya kunno kai a Gaza tana mai zargin Isra'ila da haifar da yanayin rashin tsaro a yankin Gabas ta tsakiya.

Kafar watsa labaran Tasnim ta Iran ta ba da labarin cewa a wata sanarwar da ta fitar a daren jiya Litinin, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rashan ta bayyana haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin ummul aba'isin kara dagula lamurran tsaro a Zirin Gazan da ke karkashin killacewar HKI.

Wannan sanarwar ta ma'aikatar harkokin wajen Rashan ta biyo bayan rikicin da ya barke ne a kan iyakan Zirin na Gaza da yankunan da yahudawan suka mamaye sakamakon wasu hare-hare da suka  kai Zirin na Gaza.

Shi ma a nasa bangaren babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana cewa sake kaddamar da yaki a Gaza din zai zamanto mai tsanani kuma zai haifar da gagarumin rikici a yankin.