MDD Ta Bukaci Kawo Karshen Yaki A Yemen
A wata sanarwa da ya fitar daren jiya Talata, manzon musaman na MDD kan kasar Yemen ya bukaci kawo karshen yaki a fadin kasar musaman ma a garin Hudaidah dake yammacin kasar.
Martin Griffiths ya ce dakatar da yakin shi zai ragewa al'ummar kasar ta yemen bala'in da suke ciki a yau,kuma Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wajen fara gudanar da tattaunawa tsakanin al'ummar kasar ta Yemen.
A nasa bangare, mataimakin saktare janar na MDD a al'amuran jin kai ya fitar da sanarwa a jiya talala, inda ya bukaci bangarorin dake fada da juna a kasar ta yeman su dakatar da yakin.
A yayin da yake ishara kan rusa garin Hudaidah, babban saktaren MDD António Guterres ya ce rusa wannan gari dake matsayin tashar ruwan da ake shigar da kayan agaji cikin kasar ta yemen babban bala'i ne.
Tun daga ranar 13 ga watan yuni ne kawancen Saudiya suka fara kaddamar da hare-haren sama da kasa da nufin mamaye garin na Hudaidah dake a matsayin tashar bakin ruwan yammacin kasar.