'Yan Gudun Hijirar Rohingya Sun Ki Amincewa Su Koma Myanmar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34122-'yan_gudun_hijirar_rohingya_sun_ki_amincewa_su_koma_myanmar
An fuskanci babbar matasala a ranar farko da aka sanya domin komawar tawaga ta farko ta ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya zuwa kasar Myanmar daga Bangaladesh.
(last modified 2018-11-17T06:27:55+00:00 )
Nov 17, 2018 06:27 UTC
  • 'Yan Gudun Hijirar Rohingya Sun Ki Amincewa Su Koma Myanmar

An fuskanci babbar matasala a ranar farko da aka sanya domin komawar tawaga ta farko ta ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya zuwa kasar Myanmar daga Bangaladesh.

Kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, a jiya an fuskanci matasalar komawar tawaga ta farko ta ‘yan kabilar Rohingya zuwa kasarsu ta Myanmar daga Bangaladesh kamar yadda aka tsara, saboda rashin halartar  wadanda suka kudiri aniyar komawa don kashin kansu.

An tsara a ranar jiya cewa, ‘yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira a kasar Bangaladesh da suke da bukatar  komawa Myanmar don kashin kansu da su hallara a bakin iyakokin kasashen biyu, amma babu wani daga cikinsu da ya hallara.

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira  a kasar Bangaladeh Muhammad Abu kalam ya bayyana cewa, sun halarci yankin Kokas dake kan iyaka da Myanmar tun a safiyar jiya Juma'a, amma babu wani daga cikin ‘yan gudun hijirar Rohingya da ya zo wurin.

Ya ce sun tanadi daruruwan motocin bas-bas domin jigilar ‘yan gudun hijirar zuwa Myanmar, bayan cimma matsaya kan hakan tare da hukumomin Myanmar, amma a halin yanzu wannan magana ta rushe.