MDD: Ana Shirin Gudanar Da Tattaunawa Domin warware Rikicin Kasar Yemen
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan rikicin kasar Yemen martin griffiths ya bayyana cewa, yana shirin jagorantar wani zaman tattaunawa da nufin kawo karshen rikiicin kasar ta Yemen.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoto daga birnin New York cewa, a zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya kan batun yakin Yemen, manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan rikicin kasar Yemen martin griffiths ya gabatar da rahotonsa kan halin da ake ciki dangane da shirin tattaunawa tsakanin bangarorin rikicin kasar ta Yemen.
Ya ce nan ba da jimawa ba wakilan dukkanin bangarorin siyasar kasar Yemen da ba su ga maciji da juna, za su hallara akasar Sweden, domin gudanar da tattaunawar sulhu a tsakaninsu, kuma ya zuwa yanzu dukanin bangarorin sun amince da hakan.
Dukkanin bangarori da suka hada da majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar tarayyar turai gami da sauran bangarori na kasa da kasa, suna ci gaba da kiran Saudiyya da ta dakatar da hare-harenta akan kasar ta Yemen domin bayar da dama ga 'yan kasar su zauna kan teburin tattaunawa, amma har hanzu tana ci gaba da kaddamar da hare-hare ta sama da kasa, musamman a kan brinin Hudaidaidah da ke gabar ruwa, da nufin karbe iko da shi, lamarin da har yanzu ya faskara.