An Yi Wa Jamal Khashoggi Sallar Mamaci A Kasashe Daban-Daban
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34124-an_yi_wa_jamal_khashoggi_sallar_mamaci_a_kasashe_daban_daban
A jiya ne aka gudanar da sallar mamaci ga Jamal Khashoggi dan jarida dan kasar Saudiyya, wanda aka kashe a ofishin jakadancin kasarsa a Istanbul, kuma aka batar da gawarsa.
(last modified 2018-11-17T06:28:48+00:00 )
Nov 17, 2018 06:28 UTC
  • An Yi Wa Jamal Khashoggi Sallar Mamaci A Kasashe Daban-Daban

A jiya ne aka gudanar da sallar mamaci ga Jamal Khashoggi dan jarida dan kasar Saudiyya, wanda aka kashe a ofishin jakadancin kasarsa a Istanbul, kuma aka batar da gawarsa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da sallar mamacin a masallacin Fateh da ke birnin Istanbul na kasar Turkiya, tare da halartar daruruwan jama'a.

Baya ga haka ma, an gudanar da irin wannan sallah a biranen Makka da Madina da ke kasar Saudiyyah, kamar yadda aka gudanar da irinta a birnin Washington na Amurka.

A wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho a jiya Juma'a, shugabannin kasashen Amurka da Turkiya, sun jaddada wajabcin ci gaba da bincike kan batun kisan Khashoggi, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma masu hannu a ciki.

A nata bangaren jaridar Washington Post ta wallafa wani rahoto a jiya Juma'a da ke cewa, bisa binciken da hukumar leken asirin Amurka CIA ta gudanar kan batun kisan Khashoggi, ta kai ga gano cewa Muhammad Bin Salman ne ya bayar da umarnin kashe Khashoggi