Nan Da 'Yan Kwanaki Amurka Zata Bayyana Wanda Ya Kashe Khashoggi
Nov 18, 2018 10:08 UTC
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa nan da 'yan kwanaki masu zuwa kasarsa zata yi bayyana kan wanda ya kashe dan jaridan nan Jamel Khashoggi.
Da yake sanar da hakan ga 'yan jarida, Trump ya ce nan da kwana biyu za'a fitar da cikaken rahoto kan wanda ya aikata kisan.
Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar leken asirin Amurka ta CIA, ta sanar cewa yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohamed Ben Salman ne ya bada umurnin kashe dan jaridan, koda yake Bin Salman din ya musanta hakan.
A ranar 2 ga watan Oktoba da ya gabata ne aka kashe dan jaridan mai sukan masarautar saudiyya a karamin ofishin jakadancin Saudiyyar na birnin Santambul a Turkiyya.