Ministan Tsaron Birtaniya Ya Soki Shirin Kafa Rundunar Tsaron Kungiyar Turai
Nov 20, 2018 11:44 UTC
Ministan kasar Birtaniya ya ce kafa rundunar kasashen Turai zai yi sanadiyar raunana matakan zaman lafiya da sulhu a kasashen Turai.
Yayin da yake sukan shawarar da Shugaban kasar Faransa Emanuel Maron ya gabatar na sanar da runduna kasashen Turai ,Mista Gavin Williamson ministan tsaron kasar Birtaniya ya ce har abada kasarsa ba za ta shiga cikin wannan runduna ba.
Ministan ya ce wannan shawara za ta kasance a kan takarda ne kawai, amma kasar Birtaniya ba za ta goyi bayanta ba.
A makon da ya gabata ne Shugaba Macron na Faransa ya gabatar da shawarar kafa rundunan kasashen Turai, lamarin da nan take da ya fuskanci suka daga shugaban Amurka Donal Trump.