Amurka : An Shawo Kan Wutar Dajin California
Nov 25, 2018 17:02 UTC
Jami'an kwana kwana a Amurka sun sanar da shawo kan mummunar gobarar daji data kwashe sama da makwanni tana ci a arewacin birnin California.
Sanarwa da hukumar 'yan kwana kwana ta kasar ta fitar ta ce an shayo kan gobarar mafi muni a yankin dari bisa dari.
Alkalumman da aka fitar a baya bayan nan sun nuna cewa akalla mutum 87 suka hallaka a gobarar, wacce kuma ta cinye kimanin eka 620, tare da share birnin Paradise.
An kuma bayyana cewa mutum 249 ne suka bata a yayin gobarar, a yayin da kuma dubban gidaje suka kone kurmus.
Tags