Fao Ta Yi Gargadi Akan Karancin Kayan Abinci A Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34271-fao_ta_yi_gargadi_akan_karancin_kayan_abinci_a_duniya
Hukumar abinci ta duniya wace take a karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi akan karancin abinci mai gina jiki a duniya
(last modified 2018-11-29T07:04:07+00:00 )
Nov 29, 2018 07:04 UTC
  • Fao Ta Yi Gargadi Akan Karancin Kayan Abinci A Duniya

Hukumar abinci ta duniya wace take a karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi akan karancin abinci mai gina jiki a duniya

A jiya Laraba ne hukumar ta fitar da wani rahoto wanda ya kunshi cewa; Da akwai mutane miliyan 820 a duniya da suke fama da karancin abinci mai gina jiki

Fao ta kuma cewa yadda dan'adam yake sarrafa kasa da ruwa ta hanyoyin da ba su dace ba, sun jawo raguwar yawan abincin da ake nomawa a duniya

Bugu da kari rahoton ya ce; A na samun karuwar masu fama da yunwa a duniya saboda tashe-tashen hankula, da fadace-fadace da kuma sauyin da ake samu a cikin yanayi

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutress ya ce; A tsakanin kowanne mutane 9 da akwai mutum guda wanda ba shi da isasshen abincin da zai ci.

Har ila yau rahoton ya ce; Rabin kananan yaran da suke mutuwa a duniya a yanzu saboda yunwa ce