(UNESCO) : An Sanya Reggae Cikin Jerin Al'adun Bil Adama Masu Tarihi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34276-(unesco)_an_sanya_reggae_cikin_jerin_al'adun_bil_adama_masu_tarihi
Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al'adu ta majalisar dinkin duniya, UNESCO, ta sanya wakokin Reggae na Jamaika a cikin jerin al'adun bil adama.
(last modified 2018-11-29T10:25:18+00:00 )
Nov 29, 2018 10:25 UTC
  • (UNESCO) : An Sanya Reggae Cikin Jerin Al'adun Bil Adama Masu Tarihi

Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al'adu ta majalisar dinkin duniya, UNESCO, ta sanya wakokin Reggae na Jamaika a cikin jerin al'adun bil adama.

A taron da kwararun kwamitin suka gudanar a Port Louis, babban birnin kasar Mauritius, sun amince shigar da wakokin na Reggae a cikin jerin al'adu masu tarihi, saboda gudun muwar da suka bayar wajen gwagwarmaya da bayyana shari'a ta rashin gaskia, soyaya da isar da sakon marasa galihu.

Wakokin Raggae sun haskaka a duniya ta hanyar sananan mawakin nan na Jamaika Bob Marley da wakokinsa irinsu "No Woman, No Cry" da "Stir It Up."  da dai saurensu.

Yanzu dai Raggae ya bi sahun wasu raye-raye da kide kide dama dafe dafe a cikin jerin al'adu masu tarihi na duniya.