G20 : Trump Ya Soke Ganawa Da Takwaransa Na Rasha
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34284-g20_trump_ya_soke_ganawa_da_takwaransa_na_rasha
Shugaba Donad Trump, na Amurka ya soke ganawar da aka shirya zai yi da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, a daura da taron G20 na kasashe mafiya tattalin arziki na duniya, da za'a fara yau Juma'a a birnin Buenos Aires, na Argantina.
(last modified 2018-11-30T03:55:48+00:00 )
Nov 30, 2018 03:55 UTC
  • G20 : Trump Ya Soke Ganawa Da Takwaransa Na Rasha

Shugaba Donad Trump, na Amurka ya soke ganawar da aka shirya zai yi da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, a daura da taron G20 na kasashe mafiya tattalin arziki na duniya, da za'a fara yau Juma'a a birnin Buenos Aires, na Argantina.

Trump ya bayyana a shaffinsa na Twetter cewa, ya dau wannan matakin ne bayan da kasar ta Rasha ke ci gaba da tsare jiragen ruwan Ukraine, amma ina mai maraba da duk wata tattaunawa da takwaran nawa a duk lokacin da wata dama ta samu.

Wannan dai na zuwa sa'a guda bayan da bangarorin suka tabbatar da cewa tattaunawar da shuwagannin biyu zasuyi a daura da taron na G20 a Argentina na nan daram kamar yadda aka tsara.