Araqchi: Hakurin Iran Kan 'Yarjejeniyar Nukiliya' Yana Da Karshe
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kuma babban jami'i mai kula da yarjejeniyar nukiliyan da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya ya bayyana cewa Iran tana ci gaba da ba wa kasashen Turai dama waje samar da hanyar ci gaba da aiki da yarjejeniyar nukiliyar, sai dai kuma hakurin Iran fa yana da iyaka.
Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA inda yayin da yake magana cewa har ya zuwa yanzu kasashen Turai sun gagara samo hanyar musayen kudaden da Iran bayan takunkumin da Amurka ta sanya wa kasar, ya bayyana cewar wajibi ne a kiyaye manufofin Iran a cikin yarjejeniyar.
Sayyid Araqchi ya ce Iran za ta ci gaba da ba wa kasashen Turai din dama wajen ganin an samo wadannan hanyoyi da za a iya lamunce mata manufofinta kamar yadda yarjejeniyar ta kumsa, sai dai yace hakurin Iran a wannan fagen fa yana da iyaka.
Tun dai bayan da Amurka ta sanar da ficewarta daga yarjejeniyar nukiliyan da kuma sake kakabawa Iran takunkumin da a baya aka dage mata, kasashen Turai suka sanar da aniyarsu ta ci gaba da kiyaye yarjejeniyar da kuma samar da hanyoyin da za su lamunce manufofin Iran musamman ta bangaren kasuwanci da musayen kudade, to sai dai har ya zuwa yanzu ba a cimma gaci ba.