An Kori Ma'aikacin CNN Saboda Sukar Isra'ila
Tashar talabijin ta CNN da ke kasar Amurka, ta kori dan rahotonta saboda nuna goyon baya ga al'ummar Palastine da kuma sukar lamirin Isra'ila.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Marc Lamant Hill dan rahoton tashar CNN ne, wanda ya yi jawabi a majalisar dinkin duniya, inda a cikin jawabinsa ya kirayi kasashen duniya da su haramta duk wani abu da yashafi Isra'ila.
Haka nan kuma ya jaddada kira ga kasashen duniya da su taimaki al'ummar Palastine domin samun 'yancin kansu daga kangin Isra'ila, wanda wannan furuci ya jawo masa kora a daga aikinsa.
Bayan korarsa, Marc Lamant Hill ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, shi yana goyon bayan al'ummar Palastine, kuma yana sukar abin da Isra'ila take yi da kakkausar murya na zaluntar al'ummar Palastine tare da tauye musu hakkokinsu a cikin kasarsu.