Cibiyoyin Musulmi Masu Ayyukan Jin Kai Na Kan Gaba A Canada
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34292-cibiyoyin_musulmi_masu_ayyukan_jin_kai_na_kan_gaba_a_canada
an zabi wasu cibiyoyin musulmi biyu daga cikin cibiyoyin da suka fi kwazo a kasar Canada.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Nov 30, 2018 12:21 UTC
  • Cibiyoyin Musulmi Masu Ayyukan Jin Kai Na Kan Gaba A Canada

an zabi wasu cibiyoyin musulmi biyu daga cikin cibiyoyin da suka fi kwazo a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an zabi cibiyoyin IRDF da kuma Islamic Relief Canada a cikin kungiyoyin 100 da suka fi kwazo a kasar baki daya.

Wadannan kungiyoyi dai suna gudanar da ayyukan jin kai ne da kuma taimakon marassa galihu a ckin kasar ta Canada da ma wasu kasashen duniya.

An gudanar da zaben ne tsakanin kungiyoyin jin kai sama da dubu 86 dake kasar Canada wadanda suke gudanar da ayyukan taimako a  kasar Canada da kuma kasashen duniya.

Ko shakka babu zaben wadannan kungiyoyi guda biyu na musulmi ya kara tabbatar da cewa musulmin kasar Canada suna taka gagarumar rawa wajen tabbatar wa al’ummar kasar cewa addininsu na zaman lafiya ne da taimakon dan adam ba tare da la’akari da addininsa ko akidarsa ba.