Trump Ya Bayyana Bush A Matsayin Gwarzon Amurka
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana tsohon shugaban kasar George Herbert Walker Bush wanda ya rasu a daren Juma'a da ta gabata a matsayin gwarzon shugaban Amurka.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin sakon ta'aziyyar mutuwar tsohon shugaban Amurka George Herbert Walker Bush da Trump ya aike, ya bayyana mamacin da cewa abin koyi ne ga Amurkawa baki daya, kan yadda ya karar da rayuwarsa wajen kare Amurka.
George Herbert Walker Bush ya yi shugabancin Amurka daga 1989 zuwa 1993, shi ne ya kaddamar da yaki a kan kasar Iraki a cikin shekara ta 1990 zuwa 1991, a lokacin da tsohon shugaban kasar Iraki ya mamaye kasar Kuwait.
Bush ya rasu yana da shekaru 94 a duniya, a cikin watan Afrilun wannan shekara ne matarsa barbara ta rasu tana da shekaru 73 a duniya.