Rahoto: 'Isra'ila Ta Taimakawa Saudiyya Wajen Kashe Jamal Khashoggi
Rahotanni sun bayyana cewar wani kamfanin leken asiri na haramtacciyar kasar Isra'ila ya taimaka wa gwamnatin Saudiyya wajen kisan gillan da jami'anta suka yi wa dan jaridar kasar mai sukar siyasar kasar Saudiyyan, Jamal Khashoggi, a kasar Turkiyya.
A rahoton da ta buga, jaridar New York Times ta Amurka ta bayyana cewar daya daga cikin abokan Jamal Khashoggi kana kuma dan kasar Saudiyya da a halin yanzu yake gudun hijira a kasar Kanada ya bayyana cewar wani kamfanin samar da kwayayyakin kwamfuta na haramtacciyar kasar Isra'ila ya taimakawa gwamnatin Saudiyyan wajen kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggin.
Jaridar ta jiyo Omar Abdul'aziz yana fadin cewa kamfanin na NSO Groups shi ne kamfanin da ya kirkiri wani shiri na na'urar kwamfuta wanda yake saurare da kuma nadar bayanai da sakonnin da Jamal Khashoggin yake aikewa ko kuma yake karba ta wayarsa ta hannu da kuma ba wa Saudiyya wadannan bayanan.
Omar Abdul'aziz dai ya kai karar kamfanin ne na NSO ne saboda wannan aiki na leken asirin wayoyinsu da yake da kuma mika su ga gwamnatin ta Saudiyya; wanda a cewar jaridar ta New York Times wannan lamari yana nuni da irin alaka ta kut da kut da ke tsakanin Saudiyya da haramtacciyyar kasar Isra'ilan.