Majalisar Dattijan Amurka Ta Zargi Ben Salman Da Kashe Kashoggi
(last modified Fri, 14 Dec 2018 05:17:49 GMT )
Dec 14, 2018 05:17 UTC
  • Majalisar Dattijan Amurka Ta Zargi Ben Salman Da Kashe Kashoggi

'Yan majalisar dattijai a Amurka, sun amince da gagarimin rinjaye da wani kudiri dake zargin yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammad Ben Salman, da kisan dan jaridan nan mai sukar masarautar Saudiyyar, Jamal Khashoggi.

Wannan kudrin dai ya yi hannun riga da ikirarin shugaban kasar ta Amurka, Donald Trump, na kare Mohammad Ben Salman da hannu a kian dan jaridan.

Haka zalika 'yan majalisar dattijan sun bukaci kawo karshen duk wani irin taimakon soji na Amurkar ga Saudiyya a yakin da take jagoranta a kasar Yemen.

Saidai kudurorin biyu da 'yan majalisar na bangaren demokrate da 'yan repablicain suka amince da shi, na fuskantar kalubale, kasncewar sai akalla a watan Janairu na shekara mai shirin kamawa, za'a tattauna kansu a majalisar wakilai, a daidai lokacin sabin wakilan majalisun zasu kama aiki, sannan da wuya su samu sanya hannu shugaba Trump wanda ke da dangantaka ta kud-da-kud da Saudiyya.

Saidai duk da hakan ana ganin matakin yana da karfin gaske kuma ya nuna matukar bacin ran 'yan majalisar dattijan na Amurka game da kisan dan jaridan Kashoggi da kuma zubar da jinin da Saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen.