Kisan 'Yan Jarida Ya Karu A Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34484-kisan_'yan_jarida_ya_karu_a_duniya
Kungiyoyin kare 'yan jarida na ci gaba da nuna damuwa akan yadda kisan 'yan jarida ya karu a duniya, bayan sabon rahoton da kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa (Reporters Without Borders) ta fitar.
(last modified 2018-12-19T05:52:32+00:00 )
Dec 19, 2018 05:52 UTC
  • Kisan 'Yan Jarida Ya Karu A Duniya

Kungiyoyin kare 'yan jarida na ci gaba da nuna damuwa akan yadda kisan 'yan jarida ya karu a duniya, bayan sabon rahoton da kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa (Reporters Without Borders) ta fitar.

A rahoton data fitar a bana kungiyar ta (Reporters Without Borders), ta ce adadin 'yan jarida da aka kashe a cikin aikinsu ya kai 80 a cikin wannan shekara ta 2018, wanda kuma ya karu idan aka kwatanta da bara.

Wani rahoton kuma da kwamitin kare 'yan jarioda ya fitar ya ce 'yan jarida 53 aka kashe daga farkon watan Janairu 2018 zuwa 14 ga watan Disamban nan, sabanin 47 a shekara 2017 data gabata.

Bayanin ya ci gaba da cewa 34 daga cikin 'yan jaridan, shirya kashesu akayi, ciki har da dan jaridan na Saudiyya Jamal Khashoggi.

Haka kuma kungiyar ta nuna damuwa akan yawan 'yan jarida da ake jefawa kurkuku,duk da cewa an dan samu ragowa idan aka kwatanta da bara 251 a 272 zuwa 251 a 2018.

Rahotannin biyu dai sun ce har yanzu  Afganistan ce, kasar da aka fi kashe 'yan jarida a duniya.