An Tsinto Gawarwakin Bakin Haure 11 A Kudancin Spain
Jami'an tsaron gabar ruwa na kasar Spain, sun sanar da tsintar gawarwakin bakin haure 11, a gabar ruwan kundacin kasar.
Jami'an sun kuma sanar da ceto bakin haure 33 a lokacin da kwale-kwalen da suka ciki ya nutse a ruwa.
Bayanai sun nuna cewa dukkan mutanen bakin haure daga yankin kudu da hamadar sahara, wanda suka hada da maza 29 da kuma mata 4.
Dama dai an kwashe kwana biyu ana neman kwale-kwalen a tekun Alboran a tsakanin Andalousie da arewacin Morocco.
har yanzu kuma ana ci gaba da neman wasu kwale-kwale uku a yankin wanda suke dauke da mutane tsakanin 50 zuwa 55.
Alkalumman da hukumar kula da 'yan gungun hijira ta MDD, cewa da OIM, ta fitar sun nuna cewa tun daga watan Janairu na wannan shekara zuwa 16 ga watan Disamban nan, sama da bakin haure 55,000 ne suka isa a kasar ta Spain ta hanyar teku, sannan 744 daga cikinsu sun mutu a kokarin tsallakawa turai, wanda ya linka har sau uku adadin da aka samu a bara.