Sakataren Tsaron Amurka Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34505-sakataren_tsaron_amurka_ya_yi_murabus
Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis, ya sanar da yin murabus daga bakin aiki, kwana guda bayan da shugaban kasar Donald Trump, ya sanar da janye sojojin Amurka daga Siriya.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Dec 21, 2018 03:27 UTC
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Yi Murabus

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis, ya sanar da yin murabus daga bakin aiki, kwana guda bayan da shugaban kasar Donald Trump, ya sanar da janye sojojin Amurka daga Siriya.

Sai dai a cikin takardar murabus dinsa,Sakataren tsaron bai bayyana karara cewa ya yi hakan ne ba saboda batun Siriya, amma ya bayyana kawacen kasa da kasa kan yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta IS a matsayin kawance mai mahimmanci.

A fashinsa na Twitter, shugaba Trump, bai bayyana murabus din ministan ba, ya dai kawai bayyana cewa Jim Mattis zai bar aiki a karshen watan Fabrairu, kuma zai nada wanda zai maye gurbinsa nan bada jimawa ba.

A jiya ne dai Trump, ya sanar da cewa kasarsa zata janye sojojinta kimanin 2,000 data jibge a arewacin kasar Siriya.

Batun yanje sojojin na Amurka daga Siriya dai ya janyo zazzafar muhawara tsakanin manyan jami'an Amurkar da kuma kawayenta.

A wani labari kuma wani babban jami'in Amurka da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar (Wall Street Journal da New York Times) cewa gwamnatin Donal Trump na kuma shirin janye rabin sojojin 14,000 a kasar Afganistan.