Amurka Zata Janye Rabin Sojojinta Da Suke Kasar Afganistan
(last modified Fri, 21 Dec 2018 12:00:07 GMT )
Dec 21, 2018 12:00 UTC
  • Amurka Zata Janye Rabin Sojojinta Da Suke Kasar Afganistan

Shugaban kasar amurka Donal Trump ya bada umurnin a janye sojojin Amurka 7000 daga sojojin kasar dubu 14,000 da suke kasar Afganistan

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sanarwan ba zatan da shugaban ya bayar, kwana guda bayan sanarwan janye sojojin Amurka daga kasar Syriya ya bawa jami'an gwamnatin kasar Afganistan mamaki, inda wasunsu suke cewa ba wanda ya basu labarin wannan shirin.

Kafin haka dai kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada labarin cewa sojojin 5000 za'a janye daga kasar Afganistan, amma daga baya jaridar New York Times ta kara adadin zuwa 7000, kamar yadda ta nakalto daga jami'an ma'aikatar tsaron kasar.

Wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta ta fadawa reuters cewa za'a fara janyewar a cikin yan kwanaki ko makonni masu zuwa. 

Amma senata Linsey Graham, wani na kusa da shugaban Trump ya bayyana cewa janye sojojin Amurka daga kasar Afganistan zai sake maida kasar cikin hatsarin barazanar wani hari irin na 11 ga watan Satumban shekara ta 2001.

Ya ce yanayin da kasar Afganistan take ciki bai dace da janyewar sojojin Amurka daga kasar ba don yan ta'adda suna iya kaiwa ragowar sojojin Amurka a kasar hari, sannan Amurka tana iya asarar duk irin ci gaban da ta samu a kasar tun shekara ta 2001.