Ana Bukukuwan Kirsimeti A Duk Inda Kiristoci Suke A Duniya
Yau 25 ga watan Disamba kiristoci ke gudanar da bukukuwa da kuma addu'o'i a fadin duniya don murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Isa (a.s).
An gudanar da bukukun da aka saba gudanarwa a ko wace shekara a birnin Bethlaham na Palasdinu inda aka haife shi shekaru kimani 2000 da suka gabata.
Annabi Isa (as) dai yana daga cikin manya-manyan annabawan Allah wanda Allah ya aiko don shiryartar da mutane, kuma ya bashi littafin Injila wanda yake dauke da shiriyan da Allah ya bashi.
Don zagayowan wannan ranar manya-manyan jami'an gwamnatin JMI sun isar da sakonnin taya murna ga dukkanin kiristoci na cikin kasa da kuma sauran kasashen duniya saboda zagayowan wannan ranar mai muhimmanci.
Daga karshe hukumar radio da talebijin na Jumhuriyar musulunci ta Iran tana mika sakon taya murna ga dukkan mabiya addinin kirista a ko ina suke a duniya da kuma dukkan masoyan shi don zagayowan wannan rana.