Sarauniyar Ingila: Sakon Sulhu Na Al-Masihu Ba Ya Tsufa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34576-sarauniyar_ingila_sakon_sulhu_na_al_masihu_ba_ya_tsufa
Saraunyar Ingila wacce ta aike da sakon Kirsimati ta kafafen watsa labaru kamar yadda ta saba a kowace shekara ta ce; Sakon da annabi Isa ( a.s) ya zo da shi na sulhu da son aikata alheri ga duniya ba zai taba zama tsoho ba
(last modified 2019-01-16T07:30:45+00:00 )
Dec 26, 2018 07:25 UTC
  • Sarauniyar Ingila: Sakon Sulhu Na Al-Masihu Ba Ya Tsufa

Saraunyar Ingila wacce ta aike da sakon Kirsimati ta kafafen watsa labaru kamar yadda ta saba a kowace shekara ta ce; Sakon da annabi Isa ( a.s) ya zo da shi na sulhu da son aikata alheri ga duniya ba zai taba zama tsoho ba

Saraunyar ta Birtaniya ta kara da cewa; Fiye da kowane lokaci a baya, a yanzu ana da bukatar bayar da muhimmanci ga wannan sakon.

Da take magana akan batun da ake dangatawa da batun mika mulki ga danta Yarima  Charles, sarauniya Elizabetrh 2 ta ce; A wasu al'adu ana daukar cewa rayuwa mai tsawo tana tattare da hikima, ni ma abin da nake tunani kenan.

Sarauniyar ta ci gaba da cewa; Watakila yana cikin wannan irin hikimar mu fahimci sarkakiyar da take cikin rayuwar mutum, kamar yadda yake da son aikata alheri, haka nan kuma yake da halin shaidanci.

Bugu da kari jawabin na Sarauniyar ta tabo batun ficewar kasar daga tarayyar Turai, tare da yin kira ga bangarorin da suke da sabani a cikin gida da su girmama juna