Rasha Ta Zargi Amurka Da Karya Alkawali
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34589-rasha_ta_zargi_amurka_da_karya_alkawali
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana shakkunsa akan yiyuwar ficewar sojojin Amurka daga Syria
(last modified 2018-12-28T11:59:33+00:00 )
Dec 28, 2018 11:59 UTC
  • Rasha Ta Zargi Amurka Da Karya Alkawali

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana shakkunsa akan yiyuwar ficewar sojojin Amurka daga Syria

Lavrov ya ce; Ba kodayashe ne Amurkan take cika alkawalinta ba

Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Jordan Ayaman Safadi, ya ce; Har yanzu ba mu da cikakkiyar masaniya akan shirin da Amurkan take da shi na ficewa daga kasar Syria

Segey Lavrov ya ce; Wajbi ne mu tsaya mu ga abin da zai faru danagane da ficewar Amurkan daga kasar Syria

A makon da ya shude ne dai Amurkan ta sanar da cewa za ta fice daga kasar Syria.

Wani labarin da dumi-duminsa daga Syria ya ce sojojin kasar Syria sun shuga cikin garin Manbaj na Kurdawa. 

Tashar talabijin din almayadeen ta ce; An daga tutocin kasar Syria a cikin sassa daban-daban na birnin, sai dai an ga jiragen yakin Amurka suna shawagi a sama