Trump Zai Jinkirta Janye Sojojin Amurka Daga Siriya
(last modified Mon, 31 Dec 2018 04:27:50 GMT )
Dec 31, 2018 04:27 UTC
  • Trump Zai Jinkirta Janye Sojojin Amurka Daga Siriya

Wani dan majalisar dattijai na jam'iyyar republican a Amurka kuma na kusa da shugaba Donald Trump, mai suna Lindsey Graham, ya bayyana cewa Trump a shirye yake ya jinkirta shirin janye sojojin kasarsa daga Siriya.

Sanata Graham, wanda dama yana cikin wandanda suka nuna matukar damuwa kan matakin, ya bayyana hakan ne ga 'yan jarida bayan kammala wata liyafar cin abinci da Shugaban.

Ya ce Trump ya bashi tabbacin cewa koda zasu fice daga Siriya to sai sun samu tabbaci akan cewa an murkushe kungiyar (IS).

A 'yan kwanakin da suka gabata ne shugaban na Amurka ya sanar da shirinsa na janye sojojin kasarsa kimanin 2,000 dake Siriya.

Shi dai Trump ya dauki wannan matakin ne duk da cewa manyan jami'an soji na Amurka sunyi masa da kashedi akan gaggauta hakan, wanda a cewarsu zai karawa manyan kawayen Siriya da suka hada da Rasha da kuma Iran karfi ne.

A don haka sanatan ya bukaci, Trump da ya zauna da manyan jami'an sojin kasar domin tsara yadda zasu janye sojojin.

Kasashe dai irinsu Iran sun bayyana shigar Amurka a Siriya tunda farko ma a matsayin kuskure..