Sheikh Hasina Ta Lashe Zaben Bangladesh
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34622-sheikh_hasina_ta_lashe_zaben_bangladesh
Hukumar Zaben Bangladesh ta sanar da sakamakon zaben kasar wanda ya nuna fira minista Sheikh Hasina a matsayin wadda ta lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi.
(last modified 2018-12-31T04:53:41+00:00 )
Dec 31, 2018 04:53 UTC
  • Sheikh Hasina Ta Lashe Zaben Bangladesh

Hukumar Zaben Bangladesh ta sanar da sakamakon zaben kasar wanda ya nuna fira minista Sheikh Hasina a matsayin wadda ta lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi.

Wannan dai shi ne karo na uku da fira ministar kasar Sheikh Hasina ke lashe zaben tun shekarar 2009 da ta ke rike da madafin iko a wannan kasa ta Bangladesh data kunshi mafi yawan al'umma musulmi.

Sakamakon ya nuna Sheikh Hasina ta lashe zaben da gagaromin rinjaye inda ta samu kujeru 288 cikin 300 da majalisar ta kunsa, a yayin da babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta samu kujera shida kawai.

Tuni dai jam'iyyun adawa suka yi fatali da sakamakon zaben wanda suka ce yana cike da magudi.

Jagoran jam'iyyar adawa ta kasar, Kamal Hossain, ya bukaci hukumar zaben kasar data soke zaben, tare da bukatar a sake gudanar da zaben a karkashin wata gwamnatin rikon kwarya inji shi.

Dama dai akwai 'yan takara 47 da suka janye daga tsayawa takara daf da a kammala kada kuri'a, bayan da suka yi zargin an tafka magudi.

A nata bangare hukumar Zaben kasar ta ce lalle ta samu rahotanni daga sassa daban-daban na kasar da ke cewa an tafka magudi, kuma ta ce za ta bincike lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa an samu tashin hankali a yayin kada kuri'a a zaben na jiya inda akalla mutum 17 suka rasa rayukansu.

Sheikh Hasina, mai shekaru 71, 'ya ce ga Sheikh Mujibur Rahman, shugaban kasa na farko na kasar ta Bangladesh.