Trump: Za'a Ci Gaba Da Dakatar Da Ayyukan gwamnati
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddada matsayinsa na cewa za'a ci gaba da dakatar da ayyukan gwamnatin tarayyar kasar, har zuwa lokacinda majalisar dokokin kasar ta bada kudaden gina katanga tsakanin kasar da kasar Mexico
Muryar JMI ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma'a, bayan ganawarsa da wasu yan majalisar wakilan kasar daga jam'iyyar Democrats a fadar White House.
Shugaban ya kara da cewa gina katanga a kan iyakar kasar da kasar Mexico yana bukatar dalar Amurka billiyon 5.6, kuma manufar ginata ita ce hana yan ta'adda shiga kasar.
Kafin haka dai dan majalisar dattawan kasar ta Amurka dan jam'iyyar Democrates Chark Chumer ya yi kira ga shugaba Donal Trump ya kawo karshen dakatar da ayyukan gwamnati da yake yi, don hakan yana cutar da mutanen Kasar.
Masana sun bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka kanta tana asarar dalar Amurka biliyon daya da miliyon 200 a ko wani mako sanadiyyar rufe ofisoshin gwamnatin tarayyar a bangaren kudaden shiga kawai.
Cibiyar gwaje-gwajen ra'ayin jama'a ta Standsrd & Poor's ta ce, dakatar da ayyukan gwamnati a kasar ta Amurka ya jawo karuwan rashin aikin yi da kuma rashin biyan albashi na ma'aikata kimani dubu 800.