Shugaban Venezuela ya Yi Allawadai Da Shishigin Amurka A Lamuran Kasarsa
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro ya yi rantsuwara kama aiki a matsayin shugaban kasar Venezuela karo na biyu a jiya Alhamis.
Majiyar muryar JMI daga Caravas ta bayyana cewa shugaba Madoro ya zargi kasashen Amurka da kuma kasashen kungiyar LIMA da yi masa zagon kasa, ya kuma bayyanasu a matsayin wadanda suke son dawo da mulkin kama karya a kasar Venezuela.
A ranar 4 ga watan Jenerun da muke ciki ne kungiyar LIMA ta kasashen yankin laten Amurka suka bukaci shugaba Madoros da ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar Venezuela don a sake zabe mai inganci a kasar, sannan sun sha alwashin cewa ba zasu taba amincewa da shi a matsayin halattaccen shugaban kasar Venezueala ba.
Shugaba Nicolas Madoro dai ya zama shugaban kasar Venezuela ne a shekara ta 2013 bayan rasuwar shuaba Hogo Cheves. Sannan aka sake zabensa a karo na biyu a shekaran da ta gabata.
Kasashenkungiyar Lima dai suna hada da Venezuelan, Agentina m Brazil, Canada, Chilli, Colombia , Costorica, Gwatamala, Hundurus, Panama, Paragua, Preu, Mixico da Sient KLusyo.