MDD Ta Bukaci Gwamnatin Bahrain Da Ta Saki Nabil Rajab
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34765-mdd_ta_bukaci_gwamnatin_bahrain_da_ta_saki_nabil_rajab
Majalisar dinkin duniya ta bukaci masarautar Bahrain da ta gaggauta sakin shugaban cibiyar kare hakkin bil adama na kasar da take tsare da shi.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Jan 11, 2019 17:28 UTC
  • MDD Ta Bukaci Gwamnatin Bahrain Da Ta Saki Nabil Rajab

Majalisar dinkin duniya ta bukaci masarautar Bahrain da ta gaggauta sakin shugaban cibiyar kare hakkin bil adama na kasar da take tsare da shi.

A cikin bayanin da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar duniya ya fiyar a makon da ya gabata, ya bukaci masarautar Bahrain da ta janye hukuncin da kotun kasar ta yanke kan shugaban cibiyar kare hakin bil adama na kasar Dr. Nabil Rajab, wanda kwamitin ya bayyana da cewa hukunci ne na siyasa.

Kotun kasar Bahrain ta daure Nabil Rajab ne sakamakon nuna rashin amincewarsa da hare-haren da Saudiyya take kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen, tare da kashe mata da kananan yara wadanda ba su ba su gani ba, tare da yin kira da a kawo karshen yakin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya da suka gada Amnesty Int. da kuma Human Rihts Watch da sauran, sun yi Allawadai da wannan da wannan hukunci, tare da bayyana shi da cewa hukunci ne na mulkin kama karya, kamar yadda kuma wadannan kungiyoyi suka yi tir da Allawadai kan yadda kasashen duniya suke yin gum da bakunansu a  kan irin wannan zalunci.

Masarautar Bahrain dai tana ci gaba da yin kunnen uwar shegu da wadannan kiraye-kiraye, inda ta bayyana cewa wannan lamari na cikin kuma tana dama ta yi abin da ta ga dama a cikin kasarta.