Faransa: Fiye Da Mutane Dubu 84 Suka Yi Zanga-Zanga
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34781-faransa_fiye_da_mutane_dubu_84_suka_yi_zanga_zanga
A jiya Asabar dubun dubatar mutane suka yi jerin gwano a biranen kasar Faransa sakamakon kiran da masu sanye da riguna dorawa suka yi a fadin kasar.
(last modified 2019-01-13T07:16:25+00:00 )
Jan 13, 2019 07:16 UTC
  • Faransa: Fiye Da Mutane Dubu 84 Suka Yi Zanga-Zanga

A jiya Asabar dubun dubatar mutane suka yi jerin gwano a biranen kasar Faransa sakamakon kiran da masu sanye da riguna dorawa suka yi a fadin kasar.

An gudanar da zanga-zangar a mafi yawan biranan kasar ta faransa, inda masu gangami suka sha alwashin ci gaba da yunurin nasu har sai shugaba Emmanuel Macron ya sauka daga kan shugabanci, inda suke ikirarin cewa ya gaza.

An zuba 'yan sanda kimanin dubu 80 a biranen kasar, domin murkushe zanga-zangar, inda aka yi bata kashi a  birane daban-daban tsakanin masu jerin gwanon da kuma jami'an tsaro, musamman a  birnin Paris fadar mulkin kasar.

Gwamnatin Faransa dai ta sha alwashin murkushe wannan zanga-zanga bisa hujjar cewa ta sabawa kaida, lamarin da ya kara tunzura masu zanga-zangar ci gaba da kara fitowa, da fantsama  a kan titunan manyan biranan kasar.