An Kama Wata Kungiya Wacce Take Cin Zarafin Yara A Biritaniya
Yan sanda A Kasar Biritaniya Sun Bada Sanarwan Kama Wasu Mutane Dangane Da Cin zarafin yara a wurare daban-daban a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar yansanda a kasar Britaniya tana cewa yan sandan kasar sun kama mutane 55 a wurare daban-daban na kasar wadanda suke cin zarafin yara kuma tuna an jefasu cikinn kurkuku.
Labarin ya kara da cewa an kama mutanen ne daga garuruwan 1- Dewsbury 2- Betley da kuma 3- Bradford. Labarin ya kara da cewa ana tuhumar wadanan mutane da lalata yara da zin zarafinsu tun shekara ta 2002 zuwa 2009.. Majiyar ta kara da cewa an gano wadannan mutane ne ta hanyar karar da wata mata ta shigar dangane da cin zarafinta a lokacinda take yaro a hannun wadannan mutane.