Malaman Makarantun Firamari 32,000 Suka Fara Yajin Aiki A Amurka
Jan 15, 2019 07:34 UTC
		Malaman makarantun firamari kimanin dubu 32 ne suka fara yajin aiki a birnin Los Angelis na kasar Amurka sanadiyyar karancin albashi.
Majiyar muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga birnin ta bayyana cewa tun kafin haka kungiyar malaman makarantun sun shiga tattaunawa da jami'an gwamnatin jihar kan wannan batun , amma ba tare da kaiwa da fahintar juna ba. Malaman dai suna bukatar karin kashi 6.5 % na albashinsu sannan suna bukatar a rage yawan daliban da suke karantarwa a azuzuwa.
A jiya litinin dai malaman suka soma yajin aikin, inda daliban wadannan makarantu kimani dubu 600 suka je makaranta ba tare da malamansu ba. Kuma ana saran malaman zasu ci gaba da yajin aikin a yau Talata.
