Yunkurin Hana 'Yar Majalisar Amurka Musulma Zuwa Palastine
(last modified Fri, 18 Jan 2019 16:46:33 GMT )
Jan 18, 2019 16:46 UTC
  • Yunkurin Hana 'Yar Majalisar Amurka Musulma Zuwa Palastine

Wasu yan majalisar dokokin na kokarin ganin an hana Rashida Tlaib 'yar majalisar dokokin Amurka musulma yin tafiya zuwa Palastine.

Shafin yada labarai na Dalas News ya bayar da rahoton cewa, Brain Babis dan majalisar dokokin Amurka daga jahar Texas, ya gabatar da bukata ga shugabar majlaisar wakilan Amurka, wadda ta kunshi cewa, suna yin kira da majalisar ta dauki matakin hana 'yar majalisa Rashida Tlaib yin tafiya zuwa Palastine, domin hakan zai iya kawo matsala da rashin jituwa tsakaninsu da babbar kawarsu Isra'ila.

Ya ce bai kamata wani jami'in Amurka ya tafi Palastine domin goyon bayan masu kiyayya da Isra'ila ba, domin hakan yana tattare da hadari ga makomar alaar Amurka da Isra'ila.

Tun a  cikin watan Disamban da ya gabata ne dai Rashida Tlaib wadda 'yar majalisar dokokin Amurka ce musulma kuma 'yar asalin Palastine, ta bayyana cewa za ta tafi Palastine tare da wata tawaga ta masu rajion kare hakkokin bil adama, a daidai lokacin da wata tawagar wasu 'yan majalisar dokokin za su tafi Isra'ila domin kara jaddada goyon bayansu ga Isra'ila.