Turai Ta Kakabawa Wasu 'Yan Kasuwa Da Kamfanonin Siriya Takunkumi
Majalisar kungiyar kasashen Turai ta fitar da jerin wasu 'yan kasuwa 11 da kamfanoni biyar a jerin wadanda ta kakabawa takunkumi.
Hukumar gidan radio da talabijin na kasar Iran ya nakalto Majalisar kungiyar tarayyar Turai cikin wani rahoto da ta fitar a jiyar Litinin ta yi da'awar cewa wadannan 'yan kasuwa 11 da kamfanoni biyar suna taimakawa gwamnatin kasar Siriya wajen ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta.
A halin da ake ciki yanzu, kimanin mutane 270 da kamfanoni 72 na kasar Siriya, kungiyar tarayyar Turai ta kakabawa takunkumin hana bulaguro da kuma rike dukiyoyinsu a kasarshen na Turai.
A bangare guda kuma, kungiyar tarayyar Turai ta ce tana kokari na neman hanyar siyasa wajen magance rikicin kasar ta Siriya bisa kudirin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya mai lamba 2254 da kuma yarjejjeniyar da aka cimma na birnin Ganeva a shekarar 2012.
Tun a shekarar 2011 ne ta kakabawa gwamnatin Siriya takunkumi, daga wancan lokaci zuwa yanzu, kungiyar na kakabawa duk wani dan kasuwa ko kamfani da ta zarge shi da hada kai da gwamnatin ta Siriya takunkumi.