MDD : Guteress Ya Damu Kan Rigingimu Na Tsakanin Manya Kasashen Duniya
Babban sakataren MDD Antonio Gutteres ya bayyana cewa dangantaka tsakanin kasashen Amurka da Rasha da kuma Cana tana kara tabarbarewa ta yadda hakan ya sa shi damuwa dangane da makomar duniyar na gaba.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Antonio Gutteres yana fadar haka ne a jawabin da ya gabatar a taron tattalin arzikin da ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Davos na kasar Swizland..
Babban sakataren ya kara da cewa sabani tsakanin manya-manyan kasashen ukku ya yi tsananin da ba'a taba ganin irinsa ba.
Ya ce idan an sami sabani mai tsanani irin wannan a tsakanin manya -manyan kasashen duniya, yana da hatsari danga ne da zaman lafiya a duniya.
Daga karshe babban sakataren ya bukaci kasashen duniya su rungumi tattaunawa da fahintar juna a sabanin da ke shiga tsakaninsu.
A shekara da ta gabata ce gwamnatin kasar Amurka ta shiga yakin tattalin arzikin da kasar Cana, sannan a bangare guda kuma ta sami sabani mai tsanani da kasar Rasha a bangarori da dama, wadanda suka hada yerjejeniyar makamai masu linzami wadanda suke iya daukar makaman Nukliya.