Rasha Ta Zargi Amurka Da Kokarin Yin Juyin Mulki A Venezuela
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34960-rasha_ta_zargi_amurka_da_kokarin_yin_juyin_mulki_a_venezuela
Kasar Rasha ta zargi Amurka da kokarin yin juyin mulki wa shugaba Nicolas Maduro, na kasar Venezuela, a daidai lokacin da kuma ta yi watsi da taron tattauna batun na Venezuela a kwamitin tsaro na MDD.
(last modified 2019-01-26T15:49:17+00:00 )
Jan 26, 2019 15:49 UTC
  • Rasha Ta Zargi Amurka Da Kokarin Yin Juyin Mulki A Venezuela

Kasar Rasha ta zargi Amurka da kokarin yin juyin mulki wa shugaba Nicolas Maduro, na kasar Venezuela, a daidai lokacin da kuma ta yi watsi da taron tattauna batun na Venezuela a kwamitin tsaro na MDD.

Jakadan Rasha a MDD, Vassily Nebenzia, ya ce Amurka da kawayenta na kokarin kifar da mulkin shugaba Venezuela ta hanyar juyin mulki, wanda kuma a cewarsa rikicin Venezuela, rikici ne na cikin gida.

Rasha dai bata samu yawan kuri'un da take bukata ba na hana gudanar  da taron kwamitin tsaron MDD, ba kan kasar ta Venezuela da Amurka ta kira ba.

A yayin kada kuri'a kan kiran taron, kasashen China, Afirka ta Kudu, da kuma Guinea Bissau da kuma Rashar sun kada kuri'ar kin amincewa da gudanar da taron, a yayin da kasashen yamma shida a sahun gaba Amurka, Faransa, da Burtaniya da Jamus da Belgium, da Poland da kuma Peru, tare da Koweit da Jamhuriya Deminicain suka kada kuri'ar amincewa da kiran taron na kan Venezuella a kwamitin tsaro, a yayin da kasashen Indonusiya da Ivory Coast suka zama 'yan ba ruwan mu kan batun.

A halin da ake ciki dai wasu kasashen turai da suka hada da  Faransa, Jamus da Spain sun baiwa Shugaban kasar ta Venezuela, Nicolas Maduro, wa'adin kwanaki takwas na kiran zabe ko kuma su amince da jagoran 'yan adawa na kasar, Juan Guaido a matsayin shugaban riko na kasar wanda zai shirya zabubuka nan gaba.