Al'ummar Venezuela Suna Adawa Da Katsalandan Din Amurka
Wani sakamakon sauraron ra'ayin jama'a ya nuna yadda mafi rinjayen mutanen kasar Venezuela suke adawa da katsalandan da Amurka take yi a harkokin cikin kasarsu
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya ambato sakamakon wani bincike da sauraron ra'ayin jama'a da cibiyar Hinterlaces mai zaman kanta ta gudanar wanda sakamakonsa ya bayyana cewa; kaso 86% na mutanen kasar ba su yarda da tsoma bakin Amurka a harkokin cikin gidansu ba
Bugu da kari kaso 81% na wadanda aka saurari ra'ayin nasu sun nuna kin amincewa da takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakabawa kasar tasu.
A cikin watan Mayu na shekarar 2018 da ta gabata ne dai aka zabi Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasa.
A makon da ya shude ne dai shugaban Majalisar dokokin kasar ta Venezuela Juan Guaido ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasar, lamarin da ya bude sabon shafin dambaruwar siyasa a cikin kasar
Shugaban kasar Amurka Donald Trump da ministansa na harkokin wajen Mike Pampeo sun nuna cikakken goyon bayansu ga Juan Guaido tare da daukarsa a matsayin shugaban kasa.