Juncker:Ba Za Mu Yarda Da Yiwa Yarjejeniyar Brexit Kwaskwarima Ba
Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai EU, sun jaddada cewa ba za su sake ganawa da Birtaniya, kan bukatar yi wa yarjejeniyar Brexit kwaskwarima ba.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Jean-Claude Juncker, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar turai a jiya laraba na fadawa Piraministan Birtaniya Theresa May yarjejjeniyar Brexit ita ce hanya mafi dacewa ga kungiyar tarayyar turai, kuma ba za mu amince da yi mata kwaskwarima ba.
Wannan mataki da kungiyar EU din ta dauka, na zuwa dai dai lokacin da Firaminista Theresa May, ke shirin sake tunkarar kungiyar da zummar, yi wa yarjejeniyar Brexit gyara.
Aranar Talatar da ta gabata ce, ‘yan majalisar Birtaniya suka kada kuri’ar goyon bayan sake tattaunawa kan Yarjejeniyar rabuwa da kungiyar kasashen Turan, da Firaminista Theresa May ta cimma da shugabannin na EU a karshen shekarar bara.
A watan Disambar bara ‘yan majalisar na Birtaniya, suka yi watsi da yarjejeniyar da Theresa May ta cimma da kungiyar kasashen Turan, amma daga bisani ‘yan majalisar suka yanke shawarar ba da damar sake tattaunawa kan yarjejeniyar.
Majalisar Birtaniyar, ta nuna rashin gamsuwa da matsayin kan iyakar yankin arewacin Ireland, iyakar da yarjejeniyar ta nuna za ta ci gaba da zama a karkashin kungiyar ta EU na gudanar da kasuwancin bai daya da kuma damar shige da fice ba tare da wasu sabbin ka’idoji ba, bayan kammala ficewar Birtaniya daga kungiyar.
Theresa May ta ce tabbas ta na fuskantar gagarumin kalubale kafin samun nasarar gamsar da shugabannin EU su amince da bukatar ta yi wa yarjejeniyar ta Brexit kwaskwarima, wadda aka shafe watanni 18 kafin cimma matsaya akanta.