Kasar Venezuela Ta Zargi Amurka Da Kokarin Haddasa Yakin Basasa
Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Jorge Arreaza ne ba yi wannan zargi a wata hira da tashar talabijin din aljazeera ta yi da shi.
Jorge Arreaza ya kara da cewa; shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya ba da umarni ga kai da momowar 'yan adawar siyasar kasar da kuma wasu kasashen yankin Latin
Ministan harkokin wajen kasar ta Venezuela ya jaddada cewa; Matakin bayan nan da kasashen turai su ka dauka akan Venezuela yana cin karo da dokokin kasa da kasa, sannan ya kara da cewa; Hakan yana a matsayin aiki ne da umarnin Washington
Bugu da kari ministan harkokin wajen kasar ta Venezuela ya ce; Gwamnati a shirye take ta bude tattaunawa da madugun 'yan adawa, Juan Guaido, haka nan kuma duk wata tattaunawa da za ta kai ga warware rikicin
Jorge Arreaza ya yabawa kasashen Uruguay da Mexico da suke goyon bayan tattaunawa domin warware dambaruwar siyasar kasar.
Nicolas Maduro ya lashe zaben da aka gudanar a watan Mayu na 2018 domin yin wani zango na shekaru 6.
A ranar 23 ga watan Janairu ne jagoran 'yan adawar aksar Juan Guaido ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela. Kasashen Amurka da turai sun nuna goyon bayansu gare shi, yayin da wasu kasashe da su ka hada Iran, Rasha, da China suke nuna goyon bayansu ga shugaba Maduro.