An Kashe Mutum Guda A Wata Zanga-Zanga A Kasar Haiti
(last modified Sun, 10 Feb 2019 19:17:38 GMT )
Feb 10, 2019 19:17 UTC
  • An Kashe Mutum Guda A Wata Zanga-Zanga A Kasar Haiti

Mutum guda ne jami'an tsaro a kasar Haiti suka kashe a zanga-zangar tsadar rayuwa wanda mutanen kasar suka gudanar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bada labarin cewa kwanaki ukku a jere kenan masu zanga-zanga a kasar Haiti suna fita kan tituna a manya-manyan biranen kasar inda suke kokawa kan tsadar rayuwa da kuma bukatar shugaban kasa Jovenel Moise ya sauka kan mukaminsa tunda ya kasa warware matsalolin mutanen kasar.

A ranar Alhamis da ta gabata ma mutanen kasar ta Haiti sun amsa kiran jam'iyyun adawa na kasar na su fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da yadda rayuwa take da tsada a kasar. 

A cikin shekaru biyu da suka gabata mizanin tsadar kayakin bukatun yau da kullum a kasar ta Haiti ya kai kasji 15%. .Banda haka akwai ma'aikatar kididdiga ta kasar ta bada rahoto mai cewa rashin kyawun harkokin gudanarwa a kasar yana haddasa matsalolin tattalin arziki a kasar.